Daga Bello Usman.
Wani bincike da aka wallafa a wata mujallar ƙasar Amurka ya gano cewa, ƙoƙarin rage Ungulu a ƙasar India ya janyo mutuwar kusan mutum 500,000 a cikin shekara biyar.
Binciken ya ce ana kallo Ungulu a matsayin masu tsaftar muhalli saboda rawar da suke taka wa, wajen cire dabbobin da suka mutu masu ɗauke da ƙwayoyin bacteria daga muhalli, gudun kada su yaɗa cuta, inji Eyal Frank, mataimakin farfesa a Jami’ar Chicago.
Tun da daɗewa, Ungulu ta kasance cikin tsuntsayen da ake samu a ko’ina a faɗin Indiya, sai dai kuma a shekaru Goma da suka gabata Ungulun suka fara mutuwa, a sakamakon wani magani da ake amfani da shi wajen yi wa shanu magani.
A tsakiyar shekarun 1990 Ungulu ta kai miliyan 50 a ƙasar, a yayin da suka kusa ƙarewa a halin yanzu saboda wannan magani da ake yi wa shanu.
Tun bayan da aka haramta amfani da maganin (diclofenac) a 2006, ƙarewar Ungulun ta ragu a wasu yankuna, amma aƙalla dangin halittu uku sun fuskanci asara daga kashi 91-98, a cewar wani rahoto da Indiya ta fitar kan tsuntsaye a baya-bayan nan.
Mista Frank tare da wanda suka wallafa binciken Anant Sudarshan, sun kwatanta yawan mutuwar mutane a wasu lardunan ƙasar Indiya, waɗanda suka taɓa zama da tsuntsayen Ungulu da batun raguwarsu.
Sun gano cewa wasu magunguna da ake sayarwa ba dai-dai ba sun janyo ƙaruwar raguwar yawan dangin Ungulu, a inda yawan mutuwar mutane ma ya ƙaru da kashi 4 a lardunan da tsuntsaye suka taɓa rayuwa.
BBC Hausa.