Daga Bashir Gasau.
Gidauniyar dake tallafawa Marasa ƙarfi da kuma wayar da kan al’umma (Charity Support and Awareness Iniatiative), ta aike da takardar Ƙorafi ga wasu Hukumomin tsaro, a bisa abin da ta ce Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi ll, yana ayyukan da suka kasance barazana ga tsaron jihar Kano.
An miƙa takardar ƙorafin wadda, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Aliyu Ɗalhatu ya sanya wa hannu, ga rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa reshen jihar Kano, Hukumar tsaron farin kaya (DSS) da kuma hukumar tsaro al’umma ta Civil Defence.
Gidauniyar tayi ƙorafin ne, inda ta zargi Sarki Sanusi da gabatar da ayyukan da zasu zamo barazana ga tsaro da kuma zaman lafiyar jihar kano.
A cewar takardar ƙorafin, “Duk da Umarnin Kotu, na dakatar da dawo da Sarki Sanusi na biyu kan karagar Sarautar Kano, amma yana zuwa tarurrukan al’umma a sassan jihar kuma yana ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, wanda kuma hakan na iya kawo ruɗani dama tashin hankali”.
Haka kuma tayi zargin wasu gungun ‘yan daba suna bin tawagar Sarkin, lamarin da yake tada hankalin al’ummar jihar dama sanya su a cikin firgici da tashin hankali.
Adan haka ta yi fatan Hukumomin tsaro, Musamman na farin kaya (DSS), zasu bincika lamarin tare da sanya idanu akan Zirga-zirgar tasa, domin tabbatar da cewa bai kawo cikas ga zaman lafiyar jihar ba.
Haka kuma ta buƙaci Sarki Sanusi yayi biyayya ga Umarnin Kotu ta hanyar daina ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, domin tabbatar da doka da oda a jihar.
A ƙarshe Gidauniyar tayi fatan Hukumomin tsaron zasu duba ƙorafin nasu ta hanyar ɗaukar matakin da ya kamata akan lamarin, domin magance dukkan wata barazana da zata iya shafar tsaron jihar.