Daga Bashir Gasau.
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu.
Cikin girmamawa gareku shuwagabanni da Jami’o’in lafiyar na kasa ta Najeriya baki daya.
Na ɗauki alkalami na ne domin nayi kira gareku akan wani ganganci da kantafi da rayukan al’umma da naga hukumar haraji ta Najeriya tayi a wani asibiti mai zaman kansa a birnin kano wato Best Choice specialist Hospital dake unguwar Gadon Kaya kan randabawud din Tal’udu.
Wasu daga cikin marasa lafiya da wasu iyaye sun kawo wa jaridar Alfijir labarai korafi akan yadda jami’an hukumar tattara harajin suka zo tare da jam’i an tsaro da bindigogi suna musu barazana akan sai dole sun tashi sun fita daga cikin asibitin bayan bala’in da suke ciki na rashin lafiya, ga kuma sun yi yawo wurare da dama a garin Kano sun rasa inda za a iya samun gadon kwanciya musamman a bangaren larurar da ta shafi yara da jarirai sai nan ɗin!
Babban abin takaici ma shine wasu daga cikin likitoci da ke Kano da ma wasu jahohin sun tsunduma yajin aiki akan hakkokinsu, maimakon wannan hukuma tayi aiki da hankali wajen taimakawa al’umma domin jin kansu, a a sai kokari take wajen kara nakasa rayuwar wadannan marasa lafiyar dake asibitin, ko kuma ma hallaka su!
Matsalar haraji dake tsakaninku da asibiti matsala ce da ta shafe ku, ba abinda ya shafi wadanda suka zo neman lafiya asibitin bane!
Don haka muke kira ga shuwagabanni na wannan kasa ta mu mai albarka, da hukumar kare hakkin bil’adama kan wannan cin zarafin da aka yiwa Al’umma da akawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Ku kuma hukumar tattara haraji Ku dubi Allah ku canja hanyar da zaku bi wajen neman hakkinku! Domin inda hakkin ku ya kare nan fa na wasu ya fara.
Idan da ya’yanku ne ke zuwa asibitin ba na talakawa ba da ai ba zaku yi hakan ba!
Kukan Kurciya Jawabi Ne.
Sakon
Editan Jajidar Alfijir labarai
Mai Biyayya A Gareku