Daga Bashir Gasau.
Ofishin babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman a yankin Sahel, ya ce ya fara wata tattaunawa ta musamman domin nemawa yankin Sahel mafita a karo na biyu.
Tattaunawar za ta maida hankali ne akan hanyoyin da za’a magance matsalolin da suka addabi yankin, kamar yadda aka ƙaddamar da kashin na farko na tattaunawar a shekarar 2021.
Wannan shiri ya kasance haɗin gwuiwa da hukumar dake kula da harkar ci-gaba a Ofishin Majalisar ɗinkin duniya (UNDP), da kuma sashen kula da Yammacin Afirka da Sahel (UNOWAS), harma da sashen Asusun kula da ƙananan yara (UNICEF).
Manufar shirin shine ƙarfafawa Matasa gwuiwa domin samar da muhimman abubuwan ci-gaba a yankin.
Wasu daga cikin manyan ƙalubalen yankin Sahel, da tattaunawar za ta maida hankali akai sune sauyin yanayi, rashin tsaro, da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki, ta yadda za’a tsara shawarwari domin ƙara ƙaimi ga matasa musamman mata, da kuma magance musu matsalolin su dama ɗaukar nauyin buƙatun su.
Haka kuma shirin na neman inganta tallafin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke bayarwa, don ci-gaban zamantakewa da tattalin arziƙi mai ɗorewa a duk faɗin yankin Sahel.
Tattaunawar da Daraktocin Yankunan Majalisar Ɗinkin Duniya ke jagoranta, za ta binciki batutuwa huɗu masu muhimmanci a cikin makonni huɗu, wadda ta fara daga 30 ga watan Satumba zuwa 25 ga Oktobar shekarar 2024.
Tattaunawar dai ta ware wa kowanne batu keɓaɓɓen zama domin samun damar maida hankali akan sa, da kuma samar da sakamako mai kyau.