Daga Bello Usman.
Babban Maga-Takardar manyan Kotunan Jihar Kano, Alhaji Abdullah Ado Bayero Esq, na tunasar da dukkan Ma’aikatan manyan Kotunan da suka san lokacin ritayar su ya cika, su gaggauta miƙa takardar wa’adin watanni Uku.
Bayero ya ce lallai duk Ma’aikacin da ya san lokacin ritayar sa yayi ya miƙa takardar wa’adin watanni Uku wato (Three months notice of retirement), kafin ranar Jumu’a 4 ga watan Oktobar shekarar 2024.
Kuma dai tunasarwar ta shafi waɗanda suka cika shekaru 35 suna aiki wato daga shekarar 1989 zuwa 2024, ko kuma waɗanda suka cika shekaru 60 da haihuwa.
A ƙarshe takardar tunasarwar me Lamba HCS/CIR/6/T.1/25 of 20/5/24, tayi fatan waɗanda lamarin ya shafa zasu bi umarnin Babban Maga-Takardar manyan Kotunan Jihar ta Kano.