Home / Government / ‘Yancin Kai: Gina Najeriya Nauyi Ne Akan Kowanne Ɗan Ƙasa – Chidari

‘Yancin Kai: Gina Najeriya Nauyi Ne Akan Kowanne Ɗan Ƙasa – Chidari

'Yancin Kai: Gina Najeriya Nauyi Ne Akan Kowanne Ɗan Ƙasa - Chidari               Daga Bashir Gasau.

 

Wakilin Al’ummar Dambatta da Makoda a Majalisar Wakilan Najeriya, Rt. Honarabul Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya bayyana batun gina Najeriya a matsayin abinda ya ke wuyan kowanne ɗan ƙasar ba iya shugabanni ba.

Chidari na wannan bayani ne ta cikin saƙon taya murna ga al’ummar Najeriya, dangane da zagayowar ranar samun ‘yancin kan ƙasar, wadda take bikin cika shekaru 64 da samun ‘yanci daga Turawan Birtaniya.

A cewar sa “Duk da ƙalubalen matsalolin dake damun mu, kamar na tsaro, ƙaruwar rashin aikin yi dama matsalar taɓarɓarewar tattallin arziƙi, amma ina da ƙwarin gwuiwar za’a shawo kan matsalolin, matuƙar dukkan masu ruwa da tsaki suka haɗa kai wajen ceto ƙasar”.

Adan haka ya buƙaci ‘yan Najeriya da su ci-gaba da yiwa ƙasar addu’ar Allah ya kawo wa ƙasar mafita, akan matsalolin da suka dabai-baye ta musamman na matsin tattalin arziƙi.

Haka kuma ya taya ‘yan ƙasar murnar sake ganin wannan rana me ɗumbin tarihi, wadda take cike da fatan ganin kyakykyawar rayuwa ga al’ummar ƙasar a nan gaba.

A ƙarshe ya jinjinawa al’ummar yankin da yake wakilta duba da irin haɗin kai da goyon bayan da suke bashi, harma ya basu tabbacin ci-gaba da inganta rayuwar su ta hanyar bijiro da managartan ayyukan da zasu shafe su kai tsaye.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar