Daga Jazuli Zakari Panshekara.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, zai tafi ƙasar Ingila domin hutun mako biyu, wanda yana cikin hutunsa na shekara.
Mai bawa Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.
Ya ce shugaban zai yi amfani da damar wajen yin nazari a kan muhimman matakan da ya ɗauka a gwamnatinsa, musamman ta ɓangaren inganta tattalin arziki.
A ƙarshe sanarwar ta ce Shugaban Ƙasar zai dawo, domin ci-gaba da gudanar da mulki da zarar hutun ya ƙare.
BBC Hausa.