Home / Government / Tuƙin Gangancin Shugabanni Ne Ya Jefa Najeriya Cikin Mawuyacin Hali – Wazirin Hausawan Afirka

Tuƙin Gangancin Shugabanni Ne Ya Jefa Najeriya Cikin Mawuyacin Hali – Wazirin Hausawan Afirka

Tuƙin Gangancin Shugabanni Ne Ya Jefa Najeriya Cikin Mawuyacin Hali - Wazirin Hausawan Afirka                Daga Bashir Gasau.

 

Mai Girma Wazirin Hausawan Afirka, Ambasada Dakta Usman Abubakar Saraki, ya bayyana tuƙin gangancin da Shugabannin Najeriya suke yi wa ƙasar, a matsayin dalilin faɗawar ta cikin mawuyacin hali.

Ambasada Saraki ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR Hausa, albarkacin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai daga Turawan Mulkin mallaka na ƙasar Birtaniya.

A cewar Usman Saraki, “Babu shakka Ƙasata ta shiga yanayi mara daɗi tun bayan samun ‘yancin kai, a sakamakon yadda ta faɗa hannun Azzaluman cikinta kuma suke yi mata tuƙin ganganci”.

Adan haka ne ya yi kira ga ‘yan Nigeria da su ƙara mai da hankalinsu wajen yin addu’oi tare da komawa ga Allah, domin shine kaɗai zai bawa ƙasar dama al’ummar cikinta mafita ta inda ba’a tsammani.

A ƙarshe ya yi fatan Allah ya kawo ƙarshen tarin matsalolin da suka addabi talakawan Najeriya, ta yadda rayuwar su zata inganta kuma ta dawo cikin hayyacin ta.

A jiya Talata ne, Najeriya ta cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya, wanda kuma an sami Shugabanni da dama waɗanda suka jagoranci ƙasar, a waɗannan shekaru a tsarin Mulkin farar hula ko kuma na Mulkin Soja.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar