Home / Education / ‘Yancin Kai: Gwamnan Kano Ya Ɗauki Nauyin Kula Da Rayuwar Marayu 95

‘Yancin Kai: Gwamnan Kano Ya Ɗauki Nauyin Kula Da Rayuwar Marayu 95

'Yancin Kai: Gwamnan Kano Ya Ɗauki Nauyin Kula Da Rayuwar Marayu 95              Daga Bello Usman.

 

 

A ƙoƙarin sa na nuna halin Karamci da tausayi, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki nauyin kula da rayuwar marayu 95 da ke jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata liyafar cin abinci tare da yaran, waɗanda suke zaune a gidan marayu na jihar bayan rasa iyayensu, albarkacin murnar Ranar ‘Yancin Kai da aka gudanar jiya a Kano.

A cewar Gwamnan, “Ina so na shaidawa duniya cewa mun ɗauki cikakken nauyin marayu 95 da ke zaune a wannan waje, a inda za mu kula da karatunsu daga Firamare har zuwa Jami’a”.

Bugu da ƙari Sanarwar Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ta ce Gwamnan ya yi alƙawarin kula da lafiyarsu, abinci da kuma duk wasu buƙatunsu na yau da kullum a tsawon wa’adin mulkin sa.

“Yanzu kun zama yarana, kuma zan kula da ku kamar ‘ya’yana, Za ku fara jin daɗin rayuwa, Insha Allah”. in ji Gwamnan.

Ya kuma basu tabbacin samun duk wata kulawa da goyon bayan da ya dace yayin da yake kan mulki, ta yadda zasu sami damar cimma burikansu na rayuwa.

A ƙarshe sanarwar ta ce Gwamnan ya bayar da kayan abinci na miliyoyin Naira domin tallafa wa jin daɗin rayuwar marayun, tsaro da kuma samun wadataccen abinci.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar