Daga Bashir Gasau.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adama ta Declaration of Human Right (UDHR) dake jihar Kano, ta bayyana jawabin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na jiya Talata, a matsayin wani salo na tsokanar Talakawan ƙasar.
Babban Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA, inda ya ce jawabin nasa babu komai a ciki illa kalaman ƙara tunzura ‘yan ƙasar.
A cewar Galadanci, “Mun bibiyi jawabin Shugaba Tinubu na cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai, kuma mun fahimci babu komai a cikin sa sai tsokanar al’ummar ƙasar da yake yi da kansa”.
Inda sanarwar ta ƙara da cewa, “Mun yarda da batutuwan da ya taɓo kamar na biyan basussuka, yiwa Matasa tanadi, sanya hannun jari daga Turawa, harma da sake jaddada cewa yana sane da halin da ‘yan ƙasar ke ciki na matsin rayuwa.
Toh amma wanne sauyi aka samu a fannin kayan masarufi, matsalar Tsaro, ɓangaren Lafiya, rashin wutar lantarki, fannin Noma da Kiwo da sauran fannonin da suka shafi Talaka kai tsaye.
Adan haka ƙungiyar ta ce babu wani ƙwarin gwuiwar da talakan Najeriya ya ke dashi, na yarda da jawabin shugaban ƙasar a wannan hali da ake ciki.
A ƙarshe ƙungiyar tayi fatan Allah ya kawo wa talakawan Najeriya mafita, dangane da wannan hali da suke ciki na matsi da ƙuncin rayuwa.