Daga Jazuli Zakari Panshekara.
Ƙungiyoyin matasa a ƙasar Ghana sun hau kan titunan biranen ƙasar, domin yin zanga-zangar neman a sakar masu ‘yan uwan su kimanin 50, da wata kotu ta bai wa ƴan sanda damar tsare su a makon da ya gabata.
Wata zanga-zangar kwana uku ta nuna ƙin amince wa da haƙar ma’adanai a ƙasar ba bisa ka’ida ba, ta janyo arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro al’amarin da ya janyo aka kama masu zanga-zangar da dama bisa tuhumar haɗuwa ba bisa ƙa’ida ba, Mafari kenan da ƙungiyoyin matasan suka hau kan titunan biranen ƙasar.
Da safiyar yau Alhamis ne ɗaruruwan masu zanga-zangar suka yi dafifi, inda suka hau titunan birnin Accra suna neman a saki mutum 50 ɗin da ake tsare da su.
Mutanen ƙasar da dama dai sunyi Allah-Wadai da abin da ƴan Sandan da kuma kotu suka yi na tsare matasan har tsawon makonni biyu.
Ƙasar Ghana dai ita ce wadda ta fi kowacce ƙasa albarkatun gwal a nahiyar Afirka, to sai dai ƙasar tana fama da matsalar haƙar ma’adai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da yake jawo gurɓatar muhalli ciki har da koguna.