Home / Government / Gwamnatin Kano Ta Tallafawa Masu Lalurar Laka Da Kayan Kula Da Lafiyarsu

Gwamnatin Kano Ta Tallafawa Masu Lalurar Laka Da Kayan Kula Da Lafiyarsu

Gwamnatin Kano Ta Tallafawa Masu Lalurar Laka Da Kayan Kula Da Lafiyarsu          Daga Rabi’u Usman, Kano.

 

 

Sama da kayan Naira Milyan Bakwai Gwamnatin jihar kano ta bawa ƙungiyar masu lalurar Laka, domin su ci-gaba da kula da lafiyar su albarkacin ranar masu larurar laka ta duniya dake tafe.

Kwamishiniyar ma’aikatar Mata, ƙananan yara da masu buƙata ta musamman, Hajiya Aisha Lawan Saji Rano ce ta bayar da kayayyakin ga Kungiyar, inda ta ƙara musu da tallafin Naira Milyan ɗaya.

Da take jawabi, Hajiya Aisha Saji, ta bayyana cewa sun bawa ƙungiyar tallafin ne bisa sahalewar gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin suma su tabbatar gwamnatin kano ta san halin da suke ciki.

Ta ƙara da cewa masu buƙata ta musamman dama masu lalurar Laka suna yawan zuwa ma’aikatar, domin miƙa koken su na rashin kayayyakin su na amfanin yau da kullum.

Gwamnatin Kano Ta Tallafawa Masu Lalurar Laka Da Kayan Kula Da Lafiyarsu

Adan haka Gwamnatin ta samar musu kayan da suka ƙunshi Keken zama (Wheel chair) guda 20, Audugar Mata, Man tsabtace hannu, Katata, Bandeji da kayan wanke ciwo da dai sauran su.

A nasu ɓangaren, Shugabannin ƙungiyar masu buƙata ta musamman ɓangaren masu larurar laka, sun bayyana Jin daɗin su sakamakon yadda aka share musu hawayen damuwar da suka jima suna neman maganin ta.

A ƙarshe sun ce zasu yi amfani da ranar masu larurar laka, wadda majalisar Dinkin Duniya ta ware 1 ga watan December kowacce shekara, domin su baiwa mambobin Kungiyar da suke da buƙata.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar