Daga Bashir Gasau.
Kamfanin NNPC ya kuma ƙara Kuɗin Man Fetur a Najeriya.
An wayi garin Yau Laraba da sabon farashin litar man, inda ya tashi daga Naira 897 zuwa Naira 1, 030 a gidajen man kamfanin NNPC dake birnin tarayya Abuja.
Lamarin na baya bayan nan ya faru ne bayan NNPC ya yanke shawarar fita daga yarjejeniyar siyan mai daga matatar mai ta Ɗangote.
Hakan na nufin an kawo ƙarshen yarjejeniyar da tsara cewa NNPC ne kaɗai zai siyi Man Fetur ɗin Kamfanin Ɗangote.
Premium Times ta rawaito cewa ana siyar da man a gidajen man NNPC da safiyar yau kan N1,030 a Abuja.