Home / Government / A Watan Oktobar Nan Zamu Fara Aiwatar Da Mafi Ƙarancin Albashi – Gwamnan Gombe

A Watan Oktobar Nan Zamu Fara Aiwatar Da Mafi Ƙarancin Albashi – Gwamnan Gombe

A Watan Oktobar Nan Zamu Fara Aiwatar Da Mafi Ƙarancin Albashi - Gwamnan Gombe          Daga Aliyu Gerengi, Gombe.

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce Gwamnatinsa zata fara aiwatar da mafi ƙarancin albashi a watan nan da muke ciki na Oktoba.

Mataimakin Gwamnan Gombe Manassah Daniel Jatau ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a ofishin sa, jim kaɗan bayan cimma matsaya da ƙungiyar Ƙwadago (NLC), inda ya ce an cimma daidaiton ne a zaman farko.

A cewar Daniel, “Mun tattauna da ƙungiyar Ƙwadago (NLC), kuma Gwamna ya amince da fara aiwatar da mafi ƙarancin albashi daga wannan wata, ga Ma’aikatan jihar dama na ƙananan Hukumomi.

Haka kuma ya ce wannan mataki yana cikin ƙoƙarin da Gwamnatin ta ke yi wajen magancewa Ma’aikatan jihar matsalar ƙalubalen tattallin arziƙin da suke fuskanta dama inganta walwalar su.

A nasa ɓangaren Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) na jihar Gombe, Alhaji Yusuf Aish Bello ya bada tabbacin cewa, babu Ma’aikacin jihar za’a biya ƙasa da Naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Adan haka aka samar da kwamitin aiwatar da tsarin mafi ƙarancin albashin, inda aka bashi kwanaki Uku domin ya miƙa rahoton sa na ƙarshe akan abinda za’a biya Ma’aikatan jihar.

Taron ya sami halartar Shugaban Ma’aikata, Alhaji Ahmed Kasimu Abdullahi, Kwamishinan Kuɗi Alhaji Mohammed Gambo Magaji, Akanta Janar Alhaji Aliyu Yuguda da dai sauransu.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar