Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja.
Gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, yayi alƙawarin goyon bayan hukumar Almajirai da yaran da basa zuwa Makaranta (NCAOOSCE).
Gwamna Abiodun ya bayyana hakan ne, a yayin da ya karɓi baƙuncin babban sakataren hukumar na Najeriya, Dakta Muhammad Sani Idris, inda ya ce akwai buƙatar a gaggauta magance matsalar Almajirai dama yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin ƙasar.
Dapo wanda kuma shine Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Kudancin Najeriya ya ƙara da cewa, lamarin Almajirai da yaran da basa zuwa Makaranta yana cikin manufofin da ya sanya a gaba saboda yadda suke neman ɗaukin gaggawa.
A cewar Gwamnan, “Zan haɗa hannu da hukumar NCAOOSCE domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar Ogun, waɗanda suka ƙunshi kashi 10.3% na yaran da suka isa shiga makarantar firamare, kashi 12.1% na yara ƙanana da suka isa shiga ƙaramar sakandire, dama kashi 20.9% na waɗanda suka isa shiga babbar Sakandire”.
Mafari kenan da Gwamnan ya bawa hukumar gudunmuwar ofis a jihar, tare da naɗa ma’aikacin da zai tabbatar da haɗin gwuiwar a tsakanin ɓangarorin biyu.
A nasa jawabin, Shugaban hukumar dake kula da Almajirai da yaran da basa zuwa Makaranta (NCAOOSCE) ta Najeriya, Dakta Muhammad Sani Idris ya yabawa ƙoƙarin gwamnan kan harkokin ilimi, harma ya godewa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan goyon bayan da yake bawa hukumar.
Ziyarar dai ta kasance ɗamba na yunƙurin bayar da shawarwarin Hukumar a kudancin Nijeriya, da nufin shigar da Milyoyin yaran da basa zuwa makaranta da kuma gyara tsarin ilmin Almajirci a yankin.