Home / Government / Nijar: Jagoran Azbinawa Yayi Tir Da Ƙwace ‘Yancinsa Na Zama Ɗan Ƙasa

Nijar: Jagoran Azbinawa Yayi Tir Da Ƙwace ‘Yancinsa Na Zama Ɗan Ƙasa

Nijar: Jagoran Azbinawa Yayi Tir Da Ƙwace 'Yancinsa Na Zama Ɗan Ƙasa               Daga Bello Usman.

 

Jagoran ƴan tawayen Azbinawa a Nijar kuma tsohon minista a gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, Rhissa Ag Boula, ya yi watsi da matakin da shugaban gwamnatin sojin ƙasar na ƙwace ƴancinsa na zama ɗan ƙasa tare da ƙarin wasu mutane takwas.

Ag Boula, wanda makusancin Bazoum ne ya bayyana a wani bidiyo, inda yasha alwashin ci-gaba da fafutukar mayar da Nijar bisa turbar dimokraɗiyya.

Kafar yaɗa labaran Faransa ta RFI ta ruwaito Ag Boula na cewa: “Kada ku wargaza ƙasarmu, Domin a shekarar 1991 na ɗauki makamai na tsawon shekara shida domin yaƙi da tsare-tsaren gwamnatin wancan lokaci”.

“Amma ban taɓa yin iƙirari ko kiran a ɓalle daga Nijar ba, saboda Ni ɗan Nijar ne kuma zan ci gaba da zama ɗan Nijar duk halin da aka shiga, Mu ƴan Nijar ne kuma babu wanda ya isa ya canza hakan”.

Bayan juyin mulkin 2023 ne Ag Boula ya ƙaddamar da ƙungiyar Resistance Council of the Republic (CRR), mai rajin mayar da tsohon shugaban ƙasar kan mulki, wanda har yanzu yake tsare a hannun sojojin da ke mulkin ƙasar.

BBC Hausa.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar