Daga Abdoul Niamey.
Kimanin Tukwanen Shisha dubu 51, dama ɗaruruwan ton-ton na magungunan dake sanya maye aka yi bikin ƙonawa a Jamhuriyar Nijar.
Tukwane dubu 51 dama sauran kayayyakin zuƙar tabar Shisha ‘yan sanda suka cafke a unguwannin birnin Yamai, bayan da gwamnan jihar ya kafa dokar hana shan Shisha a ranar 24 ga watan Yulin 2024.
Haka kuma an kama magungunan da yawansu ya kai ton 915, bayan da aka shigo da su ta barauniyar hanya wato ba da izinin ma’aikatar kiwon lafiya ba, yayin da wasu kuma magunguna ne na jabu, sai rukuni na 3 da aka gano cewa ana siyar da su a kasuwanni a wani lokacin da wa’adin amfani da su ya riga ya wuce.
Da yake yiwa manema labarai ƙarin haske, shugaban ofishin hukumar Douane (Kwastom) na jihohin Tilabery da Yamai, Kanal Ali Hamani ya ce watanni 9 aka shafe ana farautar irin waɗannan magunguna da ke barazana ga lafiyar jama’a.
Kanal Ali ya ƙara da cewa, sun bi dukkan hanyoyin da ya kamata a shari’ance, kafin gudanar da aikin ƙona waɗannan magunguna.
Kwamishiniyar ‘yan sanda Zouera Haoussaize, ita ce shugabar Sashen kula da kare yara da mata a hukumar ‘yan sanda ta ƙasa, ta ce wannan wani yunƙuri ne da ke hangen kariya daga illolin irin waɗannan magunguna da suka mamaye kasuwannin ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, dama ƙoƙarin kare matasa daga barazanar da wannan mummunar ɗabi’a ke yi wa lafiyar Ƙwaƙwalwa.
Shima Gwamnan Yamai Janar Assoumane Harouna, wanda ya jagoranci bikin ya jinjina wa ma’aikatan, harma ya bada tabbacin ci-gaba da ƙarfafa matakan yaƙi da irin waɗannan kayayyaki, da ke cutar da al’umma dama salwantar da makomar matasa.
Magungunan jabu da waɗanda ake shigo da su ba’a kan ƙa’ida ba, wata hanya ce ta samar da maƙudan kuɗaɗe ga waɗanda suka rungumi wannan haramtacciyar sana’a, dalili kenan ake ƙara samun yawaitar kasuwannin siyar da su a ƙasashe masu tasowa duk da matakan da hukumomi ke ɗauka, da alama talauci da jahilcin jama’a na ƙara wa abin armashi.
VOA Hausa.