Daga Bashir Gasau.
A safiyar yau Talata ne, babban layin wuta na ƙasa ya sake lalacewa inda ya jefa ɗimbin mutane cikin duhu.
Hakan na zuwa ne ƙasa da sa’a 24 bayan da kamfanonin rarraba wutar lantarki a faɗin ƙasar, suka sanar da cewa layin ya lalace da misalin karfe 6:48 na yammacin ranar Litinin.
Wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki a jihar Legas Eko ya fitar, ta ce an samu matsala a babban layin ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Talata, abin da ya janyo rashin wuta ga ɗimbin mutane.
“Muna aiki tukuru tare da abokan hulɗar yayin da muke ƙoƙarin mayar da hasken wutar lantarki, kuma za mu sanar da mutane da zarar al’amura sun daidaita,” in ji kamfanin.
Shi ma kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Kaduna ya tabbatar da sake lalacewar babban layin wutar, inda ya yi alƙawarin mayar da wuta nan bada daɗewa ba.
“Muna neman afuwar kwastomomin mu kan rashin wutar lantarki a jihohin da muke hulɗa da su tun yammacin jiya Litinin, wanda kuma wannan abu ya faru ne sakamakon lalacewar babban layin wuta na ƙasa,” in ji KEDCO.
Ya ce jami’ai a kamfanin rarraba lantarki na ƙasa (TCN) na iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin al’amura sun daidaita, daga nan kuma wutar lantarki za ta koma yadda aka saba.
BBC Hausa.