Home / Labarai / Google Ya Rattaɓa Hannu Kan Yarjejeniyar Bunƙasa Ayyukan AI

Google Ya Rattaɓa Hannu Kan Yarjejeniyar Bunƙasa Ayyukan AI

Google Ya Rattaɓa Hannu Kan Yarjejeniyar Bunƙasa Ayyukan AI       Daga Jazuli Zakari Panshekara.

 

Kamfanin Google ya rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya ta amfani da ƙananan injinan makamashin nukiliya, don samar da ɗimbin makamashin da ake buƙata don bunƙasa ayyukan ƙirƙirariyar basira ta AI.

Wannan yarjejeniya ce tsakanin Google da wani kamfani mai suna Kairos Power, wanda ya zurfafa bincike kan ƙera ƙananan na’urorin dake sarrafa makamashin nukilya.

Suna shirin ƙera injina guda bakwai, amma sai bayan sun samu izini daga hukumomin Amurka.

Kamfanonin fasaha suna ƙara karkata akalarsu zuwa makamashin nukiliya, don haɓɓaka manyan cibiyoyin gudanar da ayyukan AI.

BBC Hausa.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar