Home / Business / NASSI Da BOI Sun Sanya Hannu Akan Yarjejeniyar Bawa Ƙananan Masana’antu Rancen Bilyan 75

NASSI Da BOI Sun Sanya Hannu Akan Yarjejeniyar Bawa Ƙananan Masana’antu Rancen Bilyan 75

NASSI Da BOI Sun Sanya Hannu Akan Yarjejeniyar Bawa Ƙananan Masana'antu Rancen Bilyan 75                Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar masu ƙanana da matsakaitan Masana’antu ta Najeriya, wato Nigeria Association of Small Scale Industrialists (NASSI), ta sanya hannu akan wata yarjejeniya da Bankin Masana’antu wato Bank of Industry, wadda ta sahale a bawa Mambobin ƙungiyar rancen naira Bilyan 75.

Shugaban NASSI na ƙasa Chief Dakta Solomon Daniel Vonfa ne ya sanya hannu akan takardar yarjejeniya, a inda shi kuma Manajan Daraktan Bankin Dakta Olasupo Olusi ya sanya hannu domin fara aiwatar da wannan tsari.

Da yake yiwa jaridar GTR Hausa ƙarin haske, Babban Ma’ajin Ƙungiyar NASSI na ƙasa, Dakta Abubakar Tanko Bala ya ce manufar shirin shine nema wa Mambobinta rancen da zasu inganta kasuwancin su.

Ya kuma ƙara da cewa an kasa tsarin gida Uku, ta yadda kashin farko za’a bawa masu manyan Masana’antu rancen naira Bilyan 75, sai ɓangaren su na masu ƙananan da matsakaitan Masana’antu inda suma zasu amfana da naira Bilyan 75, da kuma masu sana’oi na gida (Nano Program) su kuma zasu amfana da Naira Bilyan 50

Bugu da ƙari ƙungiyar ta bayyana matuƙar farin cikin ta, a bisa yadda Bankin ya basu tabbacin cewa sune zasu fitar da Jadawalin waɗanda zasu amfana da wannan tsari na Rancen naira Bilyan 75 ga ƙananan da matsakaitan Masana’antun dake faɗin ƙasar.

Haka kuma yarjejeniyar ta ƙunshi yadda za’a wayar da kan masu ƙananan Masana’antu dama basu bitar yadda zasu inganta kasuwancin su ko kuma Kamfanoni dake faɗin ƙasar.

A cewar Dakta Tanko, “Wannan shiri na cikin Kyawawan ƙudirrikan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na nemawa talakawan ƙasar mafita a sakamakon irin halin da aka tsinci kai a ciki na matsi da taɓarɓarewar tattalin arziƙi”.

Adan haka ne ƙungiyar ta buƙaci dukkan Mambobin ta dake Jihohin Najeriya 36 da babban birnin tarayya Abuja su yi gaggawar shiga wannan tsari domin ya zamana sun ci gajiyar shirin ta yadda zasu bunƙasa harkokin kasuwancin nasu dama tattallin arziƙin ƙasar.

A ƙarshe Babban Ma’ajin ƙungiyar yayi fatan dukkan waɗanda suka sami wannan rance zasu yi amfani dashi ta hanyar da ta dace, kuma su dawo dashi cikin wannan lokaci da aka ƙayyade.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar