Home / Education / Ranar Matan Karkara Ta Duniya 2024: WOFAN Ta Buɗe Wasu Ayyukan Ban Mamaki Na Tallafawa Mata Da Masu Buƙata Ta Musamman

Ranar Matan Karkara Ta Duniya 2024: WOFAN Ta Buɗe Wasu Ayyukan Ban Mamaki Na Tallafawa Mata Da Masu Buƙata Ta Musamman

Ranar Matan Karkara Ta Duniya 2024: WOFAN Ta Buɗe Wasu Ayyukan Ban Mamaki Na Tallafawa Mata Da Masu Buƙata Ta Musamman              Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar dake tallafawa Mata Manoma ta Najeriya WOFAN, ta buɗe wasu ayyukan ban mamaki da ta gudanar a jihohi goma na Nigeria, inda na jihar Kano ya kasance a garin Dumaji na yankin Yadakwari dake ƙaramar hukumar Garun Malam.

Shugabar Ƙungiyar Ta Najeriya, Hajiya Dakta Salamatu Garba ce ta jagoranci buɗe ayyukan, albarkacin ranar Matan Karkara da kuma Ranar Abinci ta Duniya da ake gudanarwa a tsakanin ranar 12 zuwa 16 ga watan Oktobar kowacce shekara.

Ayyukan ta ƙungiyar ta buɗe sun haɗar da aikin borehole me kawuna goma sha uku (13) mai amfani da hasken rana, samar da Injinan chasa dana sarrafa kayan Gona cikin sauƙi, buɗewa mata wajen sarrafa kayan gona dama injin busar da amfanin gona mai amfani da hasken rana, wanda ya ke busar da su cikin kwana ɗaya ko biyu.

Ranar Matan Karkara Ta Duniya 2024: WOFAN Ta Buɗe Wasu Ayyukan Ban Mamaki Na Tallafawa Mata Da Masu Buƙata Ta Musamman Injin Busar da amfanin Gona Me amfani da hasken rana

Sauran ayyukan sune bada tallafin Babur me caji ga shugabannin masu buƙata ta musamman guda huɗu, dama samar da wajen ayyukan masu bukata ta musamman dan samun kudin shiga, wanda ya ƙunshi yin kawunan yin cajin waya har guda 120 da sauran kayan caji, kamar na babura, sannan da sana’ar POS dama gyaran Waya.

Ranar Matan Karkara Ta Duniya 2024: WOFAN Ta Buɗe Wasu Ayyukan Ban Mamaki Na Tallafawa Mata Da Masu Buƙata Ta Musamman                      Baburan masu dako da lodi 

Da take jawabi a yayin taron, Dakta Salamatu Garba ta ce sun ɗauki matakin tallafa musu ne, biyo bayan yadda masu buƙata ta musamman ɗin dake cikin su suke ƙyamatar yin bara ta hanyar rungumar sana’oin dogaro da kai.

Ranar Matan Karkara Ta Duniya 2024: WOFAN Ta Buɗe Wasu Ayyukan Ban Mamaki Na Tallafawa Mata Da Masu Buƙata Ta Musamman             Kawunan Famfo masu amfani da hasken rana

A cewar Shugabar Ƙungiyar, “Yanzu haka masu buƙata ta musamman ɗin yankin sun yi noman su da kansu, bayan mun basu tallafin Iri da Taki a inda yanzu haka sun sami abinda zasu kula da rayuwar su harma su taimaki cikakkun masu lafiya”.

Ranar Matan Karkara Ta Duniya 2024: WOFAN Ta Buɗe Wasu Ayyukan Ban Mamaki Na Tallafawa Mata Da Masu Buƙata Ta Musamman                      Injin Casar amfanin Gona

A nasa ɓangaren Sarkin Yadakwari, Alhaji Muhammad Ibrahim ya ce babu abinda zasu ce da ƙungiyar WOFAN sai godiya, duba da yadda ta samarwa al’ummar yankin kayan da zasu canza rayuwar su kuma su inganta tattallin arziƙin yankin.

Ranar Matan Karkara Ta Duniya 2024: WOFAN Ta Buɗe Wasu Ayyukan Ban Mamaki Na Tallafawa Mata Da Masu Buƙata Ta Musamman                Baburan Masu Buƙata Ta Musamman

Suma waɗanda suka amfana da tallafin ƙungiyar ta WOFAN sun bayyana matuƙar godiyarsu, inda suka yi alƙawarin yin amfani da kayan ta hanyar da ta dace.

A ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga sauran al’umma da su dinga tunawa da na ƙasan su ta hanyar taimaka musu, la’akari da cewa ba dabarar su ce ta kaisu matakin da suke kai ko kuma damar da take hannunsu ba.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar