Daga Murtala A. Baba.
Babban Mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Kano akan waka da wallafa, Honarabul Tijjani Husaini Gandu ya shawarci al’ummar jihar Kano da su ƙara haƙuri da juriya, a bisa yanayin da suka samu kansu a ciki na matsi da ƙuncin rayuwa.
Tijjani Gandu ya yi wannan kira ne a yayin zantawar sa da manema labarai a Kano, inda ya ce sannu a hankali gwamnan jihar Kano yana cika alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
A cewar Gandu, ” Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, yana sauke nauyin da yake wuyan sa, na samar da ayyukan ci-gaba da bayar da tallafi ga iyaye mata da matasa don ganin sun dogara da kansu”.
Adan haka ya bawa Kanawa tabbacin cewa Gwamnan Kano zai cika dukkan alƙawuran da ya ɗauka, domin shi mai tausayin alummar sa ne dama kishin samarwa Jihar Kano ci-gaba me ɗorewa.
A ƙarshe ya buƙaci ‘yan uwan sa Mawaka da Mawallafa da su bi sannu a hankali, ta yadda kowa zai samu rabonsa ta ɓangaren sa da kuma ta ɓangaren gwamnati.