Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja.
Hukumar kula da Ilimin Almajirai da Yaran da basa zuwa Makaranta ta Najeriya (NCAOOSCE), za ta ƙulla yarjejeniyar yin aiki tare da Gidauniyar tallafawa marasa ƙarfi ta (GBNI).
Babban Sakataren hukumar na Najeriya, Dakta Muhammad Sani Idris ne ya bayyana hakan, a yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar ta GBNI a Shalkwatar hukumar dake babban birnin tarayya Abuja.
Babban Sakataren ya ƙara da cewa, sun shirya ƙulla yarjejeniyar ne a sakamakon yadda suka gamsu, da yadda Gidauniyar take aikin tallafawa marasa ƙarfi tsakanin ta da Allah.
A cewar sa, “babu shakka aikinmu yana buƙatar haɗin gwuiwa da irin su GBNI, domin aikin namu yana kamanceceniya da juna, adan haka zamu ƙulla yarjejeniyar aikin domin samarwa al’ummar mafita ta fuskoki da dama”.
A nasa ɓangaren, Uban ƙungiyar, Dakta Umar Yanda Aliyu, ya ce sun kai ziyarar ne domin su bada gudunmawa wajen kauda mummunar fahimtar da ake yiwa harkar Almajirci.
Yanda Aliyu wanda shi ne Babban limamin Masallacin Usman bin Affan (Masallacin Banez) dake Wuse 2 Abuja, ya ƙara da cewa zasu haɗa hannu da hukumar domin cire dukkan wasu abubuwa marasa kyau da ke faruwa a cikin harkar Almajirci domin a gudu tare kuma a tsira tare.
A ƙarshe dukkan ɓangarorin sunyi fatan wannan alaƙa da ake shirin ƙulla wa zata haifar da Ɗa me ido, ta fuskar kawo kyakykyawan canji a fannin Almajircin da ake yi a faɗin Najeriya.
Ziyarar ta gudana ne bisa jagorancin Shugabar Gidauniyar Dakata Fatima Muhammed Goni, inda ta sami halartar masu ruwa da tsakin dake ɓangarorin biyu.