Home / Labarai / Ku Ci-gaba Da Koyi Da Halayen Annabi (S A W) Na Taimako – Baba Habu

Ku Ci-gaba Da Koyi Da Halayen Annabi (S A W) Na Taimako – Baba Habu

Ku Ci-gaba Da Koyi Da Halayen Annabi (S A W) Na Taimako - Baba Habu            Daga Nazifi Bala Dukawa.

 

Shugaban Kamfanin Baba Habu Global Enterprises, Alhaji Baba Habu Mika’ilu Warure, ya buƙaci al’umma da su ci-gaba da koyi da halayen Annabi Muhammad (S A W), na taimakawa marasa ƙarfi.

Baba Habu ya bayyana hakan ne, a yayin taron Maulidin tunawa da ranar haihuwar annabi Muhammad (S A W), wanda ya gudana a harabar gidansa dake birnin Kano.

Ya ƙara da cewa taimakawa marasa ƙarfi yana da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci na tsadar rayuwa, duba da yadda al’umma suke matuƙar shan wahala wajen gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Adan haka ya shawarci al’umma da su dinga taimaka wa na ƙasa dasu dama sauran marasa ƙarfi, musamman a Asibitoci dama cikin Unguwanni.

A ƙarshe ya yi kira ga jama’ar jihar Kano dama na Najeriya, da su ci-gaban da gudanar da addu’ar neman ƙarin zaman lafiya, da kuma bawa jami’an tsaro haɗin kai wajen tabbatar da tsaro.

Taron Maulidin na bana dai shine karon farko da ‘yan uwa da Iyalan Shugaban Kamfanin suka shirya, domin nuna farin cikin su da murnar ranar haihuwar Ma’aiki Annabi Muhammad (S A W).

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar