Home / Government / Itila’in Jigawa: Gwamnonin Arewa Sun Bada Tallafin Naira Miliyan Hamsin-Hamsin

Itila’in Jigawa: Gwamnonin Arewa Sun Bada Tallafin Naira Miliyan Hamsin-Hamsin

Itila'in Jigawa: Gwamnonin Arewa Sun Bada Tallafin Naira Miliyan Hamsin-Hamsin         Daga Aliyu Gerengi, Gombe.

 

Gwamnonin Arewacin Najeriya sun bada tallafin naira Milyan 50 kowannen su, ga wadanda iftila’in gobarar Tankar mai ya shafa a jihar Jigawa.

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya sanar da hakan a yayin da ya jagoranci tawagar gwamnonin Arewacin kasar zuwa jihar Jigawa, domin yin ta’aziya dama jaje ga gwamnatin jihar dama waɗanda Iftila’in ya shafa.

A nasa bangaren gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya godewa Gwamnonin Arewacin kasar a bisa wannan tallafi da suka bayar.

Sanarwar Babban mai taimakawa Gwamnan Gombe a kafofin sada zumuntar zamani, Malam Rabi’u B. Goro ya aiko wa jaridar GTR Hausa ta ce, tawagar tayi fatan Allah ya jikan wadanda suka mutu ya kuma bawa wadanda suka jikkata lafiya.

A karshe dukkan bangarorin sunyi fatan Allah ya kare faruwar hakan anan gaba, harma suka shawarci al’umma da su dinga kauracewa wurin da tankar mai ta fadi saboda gudun irin wannan matsala.

A makon da ya gabata ne Fashewar Tankar Man ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 160, a inda mutane 70 kuma suke karbar kulawa daga wurin likitoci a Asibitoci daban-daban dake Arewacin kasar.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar