Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja.
Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta sha alwashin magance matsalar Ci da gumin Makiyaya a fadin kasar.
Mashawarcin Shugaban kungiyar na kasa kan sha’anin tsaro, Alhaji Abubakar Sardauna ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da sashen Hausa na Muryar Najeriya, inda ya ce tuni suka kaddamar da kwamitin Lauyoyi domin tunkarar matsalar gadan-gadan.
A cewar Sardauna, ” Muna zargin akwai wasu mutane da suke hada kai da wasu bata-garin jami’an ‘yan Sanda suke cutar Makiyaya, ta hanyar kama su ba bisa ka’ida ba suna sanya su saida kadarorin su domin su kawo musu kudi wato “Ci da Ceto”.
“Sai a kama mutanen mu da zargin Fashi ko kuma mallakar Bindinga amma kuma babu wata cikakkiyar hujja, duk da haka sai ayi ta karbar kudi a wurinsu ba tare da an kai su Kotu ba, wanda kuma Kotu ce kadai take da hurumin hukunta su ko kuma cin tarar su”.
Adan haka ne suka kaddamar da kwamitin Lauyoyi domin ya tunkarar matsalar, ta yadda zasu magance wannan rashin adalci da ake yiwa Makiyaya.
A karshe Shugabancin MACBAN na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Alhaji Baba Usman Ngelzarma, ya bada tabbacin yin dukkan mai yiwuwa wajen sharewa Makiyaya kasar hawayen su, musamman kan lamuran da suka jibanci tsare rayuka da dukiyoyinsu.