Home / Business / Togo Da Benin Na Samun Wutar Sa’a 24 Daga Najeriya – TCN

Togo Da Benin Na Samun Wutar Sa’a 24 Daga Najeriya – TCN

Togo Da Benin Na Samun Wutar Sa'a 24 Daga Najeriya – TCN                   Daga Bashir Gasau.

 

Manajan darakta kuma babban jami’in gudanarwa na Hukumar Rarraba wutar lantarkin Najeriya TCN, Sule Abdulaziz ya ce ƙasashen Togo da Benin suna samun wutar lantarki ta sa’a 24 daga Najeriya.

Abdul Aziz ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da tashar talabijin ta Channels a jiya Lahadi, inda ya ce suna bawa kasashen Togo da Benin da Nijar lantarki ta awa 24 kuma suna biya.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ƴan Najeriya da dama ba sa samun wutar kamar haka, sai ya ce, “Yan Najeriya na samun wuta sosai amma ba a ko’ina ba, waɗanda suke “Band A” suna samun lantarki na tsakanin awa 20 zuwa 22 a rana”.

Abdulaziz ya ƙara da cewa, “ina tabbatar muku za mu iya fara samun isasshiyar wutar lantarki nan da shekara biyar. Sabon ministan yana ƙoƙari domin tabbatar da hakan.”

Ya ƙara da cewa akwai bambanci tsakanin TCN da Nepa, “lokacin da muke Nepa, mu ne muke samar da wutar, mu rarraba, sannan mu yi kasuwancinta, amma yanzu rarraba wutar kawai muke yi,” in ji shi. Sannan ya ƙara da cewa idan aka samu tangarɗa daga babban layin ƙasar, ana ɗora musu laifi ne saboda ana musu kallon Nepa.

“Idan an samu tangarɗa ba dole ta zama daga TCN ba, domin za a iya samu a sauran ɓangarorin.”

Shugaban na TCN ya kuma bayyana lalacewar kayan aiki, a matsayin wata matsala da ke addabarsu, inda ya ce, “yawancin kayayyakin aikin da muke amfani da su sun haura shekara 50.”

A game da tsadar lantarki kuwa, Abdulaziz ya ce, wutar lantarki na da sauƙi a Najeriya, idan aka kwatanta da wasu ƙasashen Afirka irin su Burkina Faso da Senegal da Jamhuriyar Nijar.

BBC Hausa.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar