Home / Business / Dalilin Daya Haddasa Rashin Wuta A Arewacin Najeriya- TCN

Dalilin Daya Haddasa Rashin Wuta A Arewacin Najeriya- TCN

Dalilin Daya Haddasa Rashin Wuta A Arewacin Najeriya- TCN              Daga Bello Usman.

 

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya TCN ya ce tangarɗar da aka samu a layin lantarki na Ugwaji-Apir mai ƙarfin 330kV, shine sanadiyyar rashin wuta a arewacin ƙasar.

Kamfanin ya ce matsalar ta shafi yankunan arewa maso gabas, da arewa maso yamma, da wasu ɓangarori na arewa ta tsakiya.

Wata sanarwa da kamfanin na Transmission Company of Nigeria ya fitar ta ce: “Da misalin ƙarfe 4:53 na safiya ne layin lantarkin Ugwuaji-Makurɗi na biyu mai ƙarfin lantarki 330kV ya samu tangarɗa, sai aka tura lantarki mai ƙarfin megawat 243 zuwa layi na ɗaya a layin domin ci gaba da samar da wutar.

“Sai shi ma da misalin ƙarfe 4:48 na safiyar ya samu matsala, wadda ta sa aka rasa lantarki mai yawan megawat 468, a inda da misalin ƙarfe 5:17, mun sake gwada layi na ɗaya da na biyun, amma dukkansu suka sake samun tangarɗa a tare.”

A makon da ya gabata ne babban layin lantarki na Najeriya ya lalace har sau uku cikin kwana biyu, abin da ya jefa dukkan ƙasar cikin duhu.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar