Daga Bashir Gasau.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Global Community for Human Right Network (GCHRN), ta shawarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano da ya hana yakin neman zaben kananan hukumomin da ake gudanarwa a halin yanzu.
Daraktan Mulki na Kungiyar, Kwamared Tasi’u Idris (Soja) ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aiko wa jaridar GTR Hausa, inda ya ce akwai bukatar daukar matakin cikin gaggawa saboda yadda yake neman haifar da matsalar tsaro a Jihar.
A cewar Soja, “Muna bada shawara ga Kwamishinan ‘yan Sandan Kano da ya gaggauta Hana yan siyasa fitowa yakin neman zabe, duba da yadda ya fara haddasa asarar rayuka da kuma dukiyar al’umma”.
Daraktan Mulkin ya kuma kara da cewa, tuni fitowar ‘yan siyasar ta haifar da kashe wadanda basu ji ba kuma basu gani ba, saboda yakin neman zaben kananan hukumomi.
Adan haka kungiyar ta ce akwai matukar bukatar Kwamishinan ‘yan Sandan dama sauran hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa, domin magance matsalar ta yadda zasu sauke nauyin dake wuyan su na kare rayuka da kuma dukiyar al’umma.
A karshe kungiyar ta yi fatan dukkan hukumomin tsaron jihar Kano zasu dauki wannan shawara tasu, domin magance matsalar cikin gaggawa, gudun kada ta haifar da wata matsalar da ta shafi tsaron jihar gaba-daya.
A ranar 26 ga watan Oktobar nan da muke ciki ne za’a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Kano, kamar yadda hukumar Zaben Jihar KANSIEC ta ayyana.