Home / Labarai / Kotu Ta Hana Hukumar KANSIEC Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Kano

Kotu Ta Hana Hukumar KANSIEC Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Kano

Kotu Ta Hana Hukumar KANSIEC Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Kano             Daga Bello Usman.

 

Babbar Kotun tarayya dake Kano ta hana hukumar zabe ta Jihar Kano gudanar da zaben kananan hukumomin jihar.

Alkalin Kotun Justice Simon Amobeda ne ya yanke hukuncin a jiya Talata, biyo bayan karar da wani ɗan jam’iyyar APC Honarabul Aminu Tiga da Jam iyyarsa ta APC suka shigar a gaban Kotun.

Kuma dai wadanda suka yi karar sun hadar da Hukumar Zaɓen (KANSIEC), Majalisar Dokokin jihar Kano, Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Hukumar Zaɓen Najeriya (INEC), Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS, reshen jihar Kano, da kuma Kwamishinan ƴansanda na jihar Kano.

Sauran wadanda aka yi karar sune Kwamandan rundunar tsaro ta Civil Defence, Anas Muhammad Mustapha, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, Mukhtar Garba Dandago, Isyaku, Ibrahim Kunya, Shehu Na Allah Kura, Kabir Jibril Zakirai da kuma Amina Inuwa Fagge.

Tun a jiya muka baku labarin yadda kotun ta rushe shugabancin hukumar zaben ta jahar Kano bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar mata na rashin cancantar shugabannin hukumar bisa kasancewarsu ƴan siyasa masu ɗauke da katin Jam’iyyar NNPP, wanda yaci karo da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 1999.

• Sauran Hukunce-hukuncen da kotun tayi shine; Shugaban hukumar zaɓen na Kano, Farfesa Sani Lawal Malumfashi bai cancanci naɗin da aka yi masa ba saboda ba ma’aikacin gwamnatin jihar Kano ba ne wanda ke ƙasa da muƙamin mataimakin Darakta kamar yadda dokar hukumar zaɓen ta Kano ta 2001 ta tanada.

• Gamayyar shugabannin hukumar zaɓen ta Kano ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka yi wa kwaskwarima a 1999 da tanade-tanaden da suka kafa hukumar zaɓen ta Kano na 2001, saboda haka ba za su iya gudanar da zaɓe a kananan hukumomin jihar 44 ba har sai an naɗa waɗanda suka cancanta tukunna.

• Duk wasu shirye-shirye da hukumar zaɓen ta yi a baya ko kuma take yi ko shirin yi a nan gaba dangane da zaɓen ƙananan hukumomi na jihar na 2024 da suka haɗa da fitar da ƙa’idojin zaɓe, tantance ƴantakara, sayar da fom ɗin shiga takara duka haramtattu ne.

• Daga yanzu an rushe kuma an kori waɗanda ake ƙara daga muƙamansu na shugabancin hukumar zaɓen da mambobinta.

• An hana hukumar zaɓen ta Kano gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na 2024 har sai an naɗa waɗanda suka cancanta.

• An hana Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC bai wa hukumar zaɓen ta Kano kayan zaɓe dangane da zaɓen ƙananan hukumomi na 2024 da suka haɗa da jerin sunayen masu zaɓe, har sai an naɗa waɗanda suka cancanci jan ragamar hukumar.

• Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta, INEC ta yi maza ta karɓe duk wasu kayan da ta bai wa hukumar zaɓen Kano idan har ma ta yi hakan, har sai an samu shugabannin da suka cancanta a hukumar zaɓen ta Kano.

• Ka da hukumar DSS ta Kano da rundunar tsaro ta NSCDC su shiga harkar zaɓen na 2024 a ƙananan hukumomi 44 na Kano, har sai lokacin da aka naɗa mutanen da suka cancanta kamar yadda doka ta tanada.

• Waɗanda ake ƙara na biyu (Majalisar Dokokin Kano) da na uku (Kwamishinan Shari’a na Kano) su tabbatar da cewa an bi ƙa’ida wajen naɗa mutanen da suka cancanta domin shugabancin hukumar zaɓen ta Kano kamar yadda kundin tsarin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 1999 da tanade-tanaden da suka kafa hukumar zaɓen ta Kano na 2001.

BBC Hausa.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar