Daga Nazifi Bala Dukawa.
Babbar Kotun Jihar Kano me Lamba 11 dake zamanta akan titin Mila, karkashin jagorancin Mai Shari’a Justice Nasiru Saminu, tace Hukumar Hisba ta jihar bata da hurumin Kame, Bincike ko kuma gurfanar da mutum a gaban Kotu.
Justice Nasiru na bayyana hakan ne a yayin da yake yanke hukunci kan karar da Murja Ibrahim Kunya ta shigar, tana karar hukumar Hisbar, Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Asibitin Dawanau da kuma Alkalin kotun Shari’ar Musulunchi dake kwana 4.
Kuma dai Murja ta shigar da karar ne ta hannun lauyoyin ta Aliyu usman Haji da kuma Saddam musa, harma a yayin hukuncin Alkalin Kotun ya ce aikin Hisba shine Wa’azi da gyara, amma dokar da ta basu damar kama mutane cushen ta aka yi.
Haka kuma Kotun ta yi watsi da gurfanarwar da Hisba ta yiwa Murja a kotun kwana 4 inda ta ayyana cewar bata kan doka, adan haka ne ta bada umarnin a mayar mata da Wayar Salularta da kuma Katin Cirar Kudi.
Toh sai dai kuma Kotun ta umarci Murja Kunya ta biya ‘Yan Sanda da kuma Asibitin Dawanau kudi naira dubu 200 Kowannensu, sakamakon gaza fito da laifin da suka yi mata a gaban kotun.
A karshe Kotun ta umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano ya kama Murja Kunya, a duk lokacin da ta yada wani abu wanda ya saba da Addini da kuma Al’ada.