Home / Labarai / Kungiyar Mar’atussaliha Ta Afirka Ta Karrama Sarkin Kabin Argungu

Kungiyar Mar’atussaliha Ta Afirka Ta Karrama Sarkin Kabin Argungu

Kungiyar Mar'atussaliha Ta Afirka Ta Karrama Sarkin Kabin Argungu      Daga Mukhtar Haliru Tambuwal.

 

Kungiyar dake tallafawa Marayu da Zawarawa ta Afirka wato (Mar’atussaliha Widows and Orphans Initiative), ta karrama Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Yusuf Abubakar Argungu (Ajiyan Kabi Babba) a bisa hidimar da yake yiwa Marayu dama Addini gaba-daya.

Shugabar Kungiyar ta Afirka, Malama Khadeejah Mar’atussaliha ce ta jagoranci bada lambar yabon, da tallafin shugabar Kungiyar ta yankin Argungu Hajiya Mariya Muhammad Mera, domin kara zaburar dashi akan aikin alherin da yake yi.

A cewar Mar’atussaliha, “Mun bashi wannan lambar yabo ne a sakamakon irin gudunmawar da yake bayarwa, wajen farantawa Marayu dama iyayen Marayun a Masarautar Kabin Argungu, domin ganin rayuwar su ta inganta kamar ta masu Iyaye”.

A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Yusuf Abubakar Argungu (Ajiyan Kabi Babba), ya bayyana matukar godiyar sa a bisa wannan shaida ta alheri da kungiyar tayi masa, harma ya basu tabbacin ci-gaba da tallafawa Marayu da Iyayen Marayun yankin domin su kara samun walwala a rayuwar su ta yau da kullum.

Bugu da kari Ajiyan Kabi Babba ya bada tabbacin hada hannu da kungiyar domin kara bijiro da sabbin shirye-shirye, wadanda zasu taimaki rayuwar Marayu da Iyayen dake kula dasu harma da sauran marasa karfi.

Taron bada lambar yabon ya gudana ne a Fadar Sarkin Kabin Argungu wadda ke Argungun Jihar Kebbi, inda ya sami halartar ‘Yan Majalisar Sarkin, Uwayen Kasa da kuma Mambobin Kungiyar.

Kungiyar Mar’atussaliha dai tayi fice ne wajen taimakon Marayu da Iyayensu Mata, ‘Yan mata, da sauran Mabukata a wasu Jihohin Kasar nan da kuma wasu Kasashen Afirka, baya ga yadda suka kware wajen gyara zamantakewar Aure da kula da lafiyar Ma’aurata, harma da horas da sabbin Ma’auratan.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar