Daga Aliyu Gerengi, Gombe.
A yau Jumu’a ne Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayi Kacibus da abokin takarar sa, a zaben daya gaba wato Alhaji Atiku Abubakar.
Sunyi Kacibus din ne a wajen daurin auren ‘yar Sanatan Gombe ta tsakiya wato Sanata Danjuma Goje, bayan da suka shafe kusan Watanni 20 basu hadu ba.
Shugaba Tinubu ne ya zama Waliyyin Amaryar wato Fauziyya Goje, a inda tsohon Gwamnan jihar Gombe Sanata Ibrahim Hassan Dan kwambo ya kasance wakilin ango Aliyu Ahmed Dukku, harma ya bada sadaki naira Milyan daya da dubu dari biyar.
Daurin Auren ya gudana ne a Babban Masallacin kasa dake Abuja, inda ya sami halartar Shugaban majalisar Dattawa Sanata Godwills Akpabio, da Mataimakin sa Sanata Barau Jibrin, Kakakin majalisar tarayya Rt. Honarabul Tajuddeen Abbas, tsaffin shugabannin majalisar Dattawa Sanata Bokola Saraki da Sanata Ahmed Lawan.
Sauran manyan bakin sune tsohon sakataren Gwamnatin tarayya Alhaji Yayale Ahmad, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnonin Jihohin Kaduna, Katsina, Bauchi, Yobe, Nasarawa da sauran masu rike da madafun iko na sassan kasar nan.
A karshe Uban Amaryar ya jagoranci manyan baki, zuwa gidan sa dake Asokoro inda aka yi lifayar cin abinci.