Home / Business / MƊD Tayi Alƙawarin Tallafawa Najeriya Domin Ta Cimma Burikanta

MƊD Tayi Alƙawarin Tallafawa Najeriya Domin Ta Cimma Burikanta

MƊD Tayi Alƙawarin Tallafawa Najeriya Domin Ta Cimma Burikanta             Daga Bashir Gasau.

Ko-odinetan Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Mohammed Fall, ya jaddada ƙudirin ƙungiyar na tallafa wa ƙasar wajen cimma muradunta na ci-gaba mai ɗorewa (SDGs).

Fall ya ba da wannan tabbacin ne a yayin wani taron manema Labarai a jiya Alhamis a Abuja, albarkacin bikin cika shekaru 79 da shigowar Majalisar zuwa tarayyar Najeriya.

Ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai matuƙar muhimmanci, harma ya ce ƙungiyar ba za ta cimma muradun karni ba idan Najeriya ba ta cimma hakan ba, adan haka ya zama wajibi a cimma Ajandar 2030 cikin kasa da shekaru biyar domin nuna babban sakamako a wajen taron ƙoli na gaba.

A cewar Fall, “Yarjejeniyar SDG ta kunshi abubuwa Biyar, wadanda suka hadar da zaman lafiya, Tsaron duniya, kimiyya, fasahar sababbin abubuwa dama samar da goben Matasa me kyau domin mulkar duniya”.

Haka kuma Najeriya tana cikin wannan yarjejeniya, shiyasa Majalisar ta himmatu wajen ganin ta cimma burikanta na SDG ta yadda al’ummar kasar zasu amfana.

A nata jawabin, wakiliyar hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya, (UNDP) a Najeriya, Elsie Attafuah, ta ce makomar ci-gaban zai mayar da hankali ne kan kimiyya, fasaha, kirkire-kirkire da kuma na’ura mai kwakwalwa.

Ta ƙara da cewa shirin zai taimaka wa Najeriya wajen daƙile tasirin sauyin yanayi, ta hanyar rage hayaki da kuma alakanta shi da ci-gaban kasar.

A karshe shugabar ofishin ƙungiyar ƙwadago ta duniya ILO a kasashen Najeriya, Ghana, Laberiya da Saliyo, Vaneessa Phala-Moyo, ta yi alƙawarin inganta zaman lafiya a ƙasar.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar