Daga Bashir Gasau.
A kokarin da take yi na tabbatar da an gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Kano cikin nutsuwa da kwanciyat hankali, Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita a fadin jihar.
Kwamishinan Yada Labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce dokar zata fara aiki ne daga 12 na Daren Yau zuwa 6 na yammacin gobe Asabar.
Sanarwar ta ce, daukar matakin ya biyo bayan tattaunawa da hukumomin tsaro, harma Gwamnatin tayi fatan al’ummar zasu bi wannan doka sau da kafa domin bada tasu gudunmawar wajen ganin an gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.
Dokar ta shafi dai-dai-kun mutanen dake zirga-zirga a kasa da kuma na ababen hawa a dukkan kananan hukumomin jihar 44 da kuma Mazabu 484.
Toh sai dai kuma wadanda dokar bata shafa ba sun hadar da ma’aikatan zaben, sauran masu aiki na musamman kamar Jami’an tsaro, Likitoci, ‘Yan Jarida da dangogin su.
A karshe Gwamnatin ta bada tabbacin gudanar da sahihin zabe ta hanyar bin ka’idojin da doka ta tanada, ta yadda zai zama an aiwatar da shi cikin kwanciyar hankali da lumana.