Home / Labarai / Zaben Kananan Hukumomin Kano: Zauren Hadin Kan Malaman Jihar Ya Aika Sako

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Zauren Hadin Kan Malaman Jihar Ya Aika Sako

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Zauren Hadin  Kan Malaman Jihar Ya Aika Sako            Daga Bello Usman.

 

Zauren Hadin Kan Malamai da Kungiyoyin Musulunci na Jihar Kano wato (Coalition of Ulama and Islamic Organisations in Kano State), ya yi kira na musamman akan muhimmancin zaman lafiya a yayin zaben kananan hukumomin jihar da za’a yi a gobe Asabar.

Sakataren zauren Dakta Saidu Ahmad Dukawa ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce sun lura da zulumin da ake ciki game da zaben adan haka ne suka bawa dukkan bangarorin shawarwari kamar haka;

1. Jagororin siyasa da ‘yan takara su ji tsoron Allah su kaucewa ingiza mutane zuwa ga abinda zai janyo tashin hankali ko asarar rayuka, ko kuma na dukiya.

Saboda haka su tuna cewa ana gudanar da zaben ne domin samar da kyakkyawan jagoranci cikin ruwan sanyi, adan haka mayar da zaben ya zamo sanadin tashin hankali tamkar yin watsi da manufar zaben ne.

2. Al’ummar jihar Kano musamman wadanda zasu je wurin zabe da wadanda zasu wakilci ‘yan takara a matakai daban daban, su ji tsoron Allah su guji duk abinda zai janyo tashin-tashina a wurin zabe ko a dalilin sa.

3. Jami’an Tsaro su tuna da rantsuwar aikinsu da hakkokin da ke kansu, domin yin aikinsu ba tare da sani ko sabo ba ta yadda zasu tabbatar sun kwantar da duk wata fitina kafin ta ta’azzara.

4. Hukumar zabe ta tuna hakkin da yake kanta na tabbatar da adalci wajen gudanar da zabe, duba da babu abinda da yake magance fitina da tashin hankali kamar tsayar da adalci, game da zabe kuma babu wanda hakkin tsayar da adalci ya rataya a wuyansa kamar hukumar zabe.

5. Malamai da sauran al’ummar gari su dage da addu’ar neman lafiya da zaman lafiya a Jihar Kano da kuma Kasa baki-daya.

A karshe Zauren yayi addu’ar Allah yasa ayi zaben lafiya a kammala lafiya, kuma Allah ya zaba mana shugabanni na gari.

About gtrhausa

Check Also

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

Matsalar Lantarki: Ƴan Kasuwar Arewa Na Neman Diyyar Sama Da Tiriliyan Daya

       Daga Jazuli Zakari Panshekara.   Yayin da ƴan kasuwa da masu ƙananan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar