Daga Jazuli Zakari Panshekara.
Majalisar Dattawan Najeriya na duba yiwuwar maida makarantun Firamare da Sakandire hannun gwamnatin tarayyar kasar gaba-daya.
Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Lawal Adamu Usman, wanda aka fi sani da Mista La, ne ya tabbatar da hakan a zantawar sa da sashen Hausa BBC Hausa.
Mista La, wanda shine shugaban kwamitin ilimi a matakin farko na majalisar dattawan kasar ya kara da cewa, tsarin na bai-ɗaya zai maida makarantun firamaren da sakandiren hannun gwamnatin tarayya gaba-daya.
Kudirin Majalisar dai wani yunkuri ne na duba batun dubban yaran da ba sa zuwa makaranta a sassan ƙasar, da nufin gano matsalolin da ke hana su zuwa makaranta, tare da nemo hanyoyin magance su.