Daga Bashir Gasau.
Ƙungiyar masu ƙanana da matsakaitan Masana’antu ta Najeriya, wato Nigerian Association of Small Scale Industrialists (NASSI), ta bude hanyar neman rancen Naira Bilyan 75 da Gwamnatin kasar ta sahale musu.
Shugaban Kungiyar na kasa Chief Dakta Solomon Daniel Vonfa ne ya sanar da hakan, a yayin wani taron manema Labarai da ya jagoranta a Shelkwatar Kungiyar dake Babban Birnin tarayya Abuja, inda ya ce a yau suka bude shafin domin Mambobin kungiyar dama dukkan al’ummar Najeriya su amfana.
Hanyar neman rancen ita ce “https://fgnboimsmeinterventionloan.boi.ng/ ” a inda wadanda zasu nema ta hannun Kungiyar kuma zasu fara yin rijista da kungiyar ta shafin “https://portal.nassi-ng.org/”.
Da yake yiwa Jaridar GTR Hausa karin haske, Babban Ma’ajin kungiyar na kasa, Dakta Abubakar Tanko Bala, ya ce ga dukkan masu bukatar wannan rance zasu iya nema ta waccan hanya, ko kuma su ziyarci Ofishin Kungiyar NASSI mafi kusa da su.
A cewar Babban Ma’ajin, “Wuraren da zaku sami Ofishin NASSI sun hadar da Jihohin Najeriya 36 da Babban Birnin tarayya Abuja, koma dukkan kananan hukumomin kasar guda 774”.
Kungiyar ta kuma shawarci Mambobin ta dama dukkan al’ummar kasar da suyi amfani da wannan dama, domin bunkasa kasuwancin su dama samun karin kudin shiga ga kasar dama habbaka tattalin arzikin ta.
Taron manema Labaran ya sami halartar masu ruwa da tsakin Kungiyar na sassan Kasar, dama tawagar Manyan Jami’an Bankin Masana’antu na Najeriya wato Bank of Industry, karkashin Jagorancin Hajiya Amina Habu.
A ranar 16 ga watan Oktobar nan ne Gwamnatin Najeriya ta amince da bawa mambobin kungiyar rancen Naira Bilyan 75, ta hannun Bankin Masana’antu domin su bunkasa kasuwancin su dama farfado da tattalin arzikin kasar.