Daga Bello Usman.
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya amince da Naira dubu 71, a matsayin mafi karancin Albashi ga ma’aikatan Jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin da ya karbi rahoton kwamitin tantance mafi karancin Albashin, karkashin Jagorancin Shugaban Ma’aikata na jihar Kano a Ofishin sa, in da ya ce sabon mafi karancin Albashin zai fara aiki ne a watan Nuwamba me kamawa.
Sanarwar Kakakin Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ta ce Albashin jihar ya karu da Naira Bilyan 6, a inda na kananan hukumomin jihar 44 zai karu da Naira Bilyan 7 domin aiwatar da sabon mafi karancin Albashin.
A karshe Shugaban Kungiyar kwadago na jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa, ya godewa Gwamnan a bisa amincewa da mafi karancin Albashin ma’aikatan jihar, wadanda suka fi dukkan Jihohin Najeriya yawan ma’aikata.