Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci-gaba da riƙe muƙamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai koma ƙasar.
Kafin naɗa shi a muƙamin, ya kasance kwamandan runduna ta 56 da ke Jaji a jihar Kaduna.
Tun a makon da ya gabata ne rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa Janar Lagbaja yana jinya a wani asibiti a ƙasar waje bayan ta musanta rahotonnin da ke cewa ya rasu, tana mai cewa Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim ne ya maye gurbinsa a matakin riƙon ƙwarya.
Daga baya hedikwatar tsaro ta Najeriya ta musanta batun, inda ta ce “babu wani batun muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa” a tsarin aikinta.