Daga Bello Usman.
Tsohon shugaban hukumar zaɓe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta yi hattara da rungumar dukkan shawawarin da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ke bayarwa.
Farfesa Jega ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da BBC Hausa, inda ya ce shawarwarin suna ƙunshe da wasu abubuwa da za su iya jefa ƙasashe masu tasowa cikin yanayi mara kyau.
Ya kuma kara da cewa lallai akwai alfanun da ke tattare da hulɗa da irin waɗannan cibiyoyin, sai dai kuma ƙasashen da suke karɓar shawarwarin, Najeriya akwai buƙatar su yi hattara, ka da hulɗar ta jefa ƙasar cikin matsin rayuwar da za’a daɗe ba’a fita ba.
“Tun a 1992 lokacin da nake jagorantar ƙungiyar ASUU asusun lamunin na duniya ya tattara ministoci na ilimi suka yi taro a Kenya, suka ce ai Najeriya ba ta buƙatar jami’o’i, suka ce karatun da ya kamata a yi shi ne abin da suke kira “technical education” wato ilimi na fasaha da ƙere-ƙere, ba wai ilimi mai zurfi irin na jami’a ba. Irin wannan shawara da gwamnatin can baya ta yi na cikin abubuwan da suka janyo mana taɓarɓarewar ilimi a halin yanzu,” in ji shi.
Jega ya ce akwai buƙatar a yi la’akari da cewa suna bayar da shawarwari ne game da abubuwan da suke ganin za su fi amfani a gare su ba wai ga ƙasashen masu tasowa ba.
Tsohon malamin jami’ar ya ƙara da cewa daga cikin ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta akwai rashin shugabanci nagari, inda ya ce tun da aka dawo tsarin Demokraɗiyya, Jam’iyyu ba su cika tsayar da ƴan takara da suka cancanta ba domin fuskantar ƙalubale.
“Mun san lokacin da aka yi wasu tsare-tsare na tsuke bakin aljihu da ake kira “Structural Adjustement Program”, waɗanda bankunan suka kawo mana tun wurin 1992, irin tsare-tsaren da suke kawowa, su ce gwamnati ta fitar da hannunta wurin inganta rayuwar jama’a ko ba su tallafi, sai dai komai a bar shi a kasuwa, kuma yadda kasuwa ta yi haka za a yi”.
“Tun lokacin ne suke bayar da irin waɗannan shawarwari, adan haka muna kyautata zaton a Najeriya ma irin abun da suke faɗa ke nan yanzu.”
Da aka bayyana masa cewa IMF ta zare hannunta daga batun cire tallafin man fetur, Jega ya ce, “To Allahu ne mafi sani, amma dai an riga an san su, kuma an san abun da suka yi a baya kuma dabarun suna da yawa.
A karshe ya ce wani lokacin ƙeƙe da ƙeƙe za’a yi, wani lokacin cikin hikima za su gabatar da abubuwa a zo a ɗauka, daga baya su ce a’a ai ba haka ba, amma dai ayi hattara, inji Farfesa Jega.