Daga Jazuli Zakari Panshekara.
Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya ta ba da shawarar dakatar da ƙudirin yi wa haraji kwaskwarima da gwamnatin tarayyar ƙasar ke shirin yi.
Mambobin majalisar National Economic Council (NEC) sun ƙunshi gwamnoni ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
Da yake magana da manema labarai bayan zaman majalisar a yau Alhamis, Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya ce sun yanke shawarar dakatar da ƙudirin ne bayan cece-kucen da ya biyo baya “da zimmar bai wa mahukunta dama”.
A yau Alhamis ne fadar shugaban ƙasa ta ce ta aike wa majalisar dokoki ƙudirin gyaran karɓar harajin domin amincewa da shi.
BBC Hausa.