Daga Bashir Gasau. Rundunar ‘Yan Sandan jihar Borno ta gudanar da taron wayar da kai, dama bada tallafin Magani kyauta a Barikin Mashimami dake jihar. Kakakin rundunar na jihar Borno ASP Nahum Kenneth Daso ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR Hausa, inda ya …
Read More »Flooding
Adamawa: Karyewar Gadar Numan Ta Jefa Rayuwar Matafiya Cikin Mawuyacin Hali
Daga Muhammad Kwairi Waziri. Cincirindon Matafiya sun buƙaci Gwamnatin Tarayyar Najeriya dama ta Jihar Adamawa su kawo musu ɗauki, a sakamakon yadda Karyewar Gadar Numan ta jefa rayuwar su cikin mawuyacin hali. Matafiyan sun shaidawa jaridar GTR Hausa cewa suna cikin wani hali na rashin sanin inda suka dosa, duba da yadda suka wuni kuma suka kwana a …
Read More »Siye Amfanin Gona Daga Masu Kuɗi Ne Ya Jawo Tsadarsa – Manoman Nijar
Daga Bello Usman. Al’ummar Jamhuriyar Nijar sun koka da yadda kayan Amfanin Gona ke tsada, duba da har yanzu farashin abinci bai yi ƙasa ba kamar yadda ake sa rai. Lamarin ya zo ne a dai-dai lokacin da manoman ƙasar suke nuna farin cikinsu da albarkar da aka samu a daminar Bana, duk …
Read More »Cutar Kwalara Ta Kashe Mutum Bakwai A Kano
Daga Bello Usman. Ana ci-gaba da zaman makoki da alhinin rasuwar mutum bakwai waɗanda suka rasu, a sakamakon cutar kwalara da suka kamu da ita bayan sun sha ruwan wata rijiya a wani ƙauye. Bayanai na cewa lamarin ya auku ne sanadiyyar gurɓacewar ruwa sakamakon ambaliyar ruwa daga wani kudiddifi da ke …
Read More »Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Aikin Tsaftar Muhalli A Ƙananan Hukumomin Jihar
Daga Bashir Gasau. Kwamishinan Ma’aikatar Gidaje da Muhalli na jihar Bauchi, Rt. Honarabul Ɗanlami Ahmed Kawule (Barden Arewan Bauchi), ya ƙaddamar da aikin tsaftar Muhalli a ƙananan Hukumomin Jihar Ashirin. Barden Arewan Bauchi ya ƙaddamar da aikin ne a Unguwar Kobi, bisa cikakken goyon bayan Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, …
Read More »Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Sabuwar Yarjejeniyar Inganta Tsarin Shugabancin Duniya
Daga Bashir Gasau. Majalisar Ɗinkin Duniya, ta amince da sabuwar yarjejeniyar inganta tsarin shugabancin duniya. Sakatare Janar na Majalisar, Antonio Gutterres ne ya bayyana hakan, a yayin jawabin buɗe taron Shugabannin duniya a ranar 22 ga watan Satumbar Shekarar 2024, inda ya ce an tabbatar da yarjejeniyar ne saboda gaba. A cewar …
Read More »Babu Barazanar Ambaliyar Ruwa A Madatsar Ruwan Challawa Goje – MD Hadejia Jama’are
Daga Bashir Gasau. Hukumar raya Kogunan Hadejia da Jama’are ta Najeriya, ta bada tabbacin cewar babu wata barazanar faruwar ambaliyar ruwa a madatsar ruwa ta Challawa Goje (Gorge), dake ƙaramar Hukumar Ƙaraye ta jihar Kano. Manajan Daraktan hukumar me kula da Jihohin Kano, Jigawa da kuma Bauchi, Alhaji Ma’amun Da’u Aliyu ne ya …
Read More »Masu Hannu Da Shuni Ku Ƙara Taimakawa Al’ummar Maiduguri – David Sabo Kentai
Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Tsohon Darakta a hukumar raya yankin Arewa maso gabashin Najeriya, Chief David Sabo Kentai, ya buƙaci masu hannu da shuni da su ƙara ƙaimi wajen taimakawa al’ummar da Ambaliyar ruwan ta shafa a Maidugurin jihar Borno. Kentai yayi wannan kiran ne, a yayin da yake miƙa saƙon sa na jaje ga gwamnati da …
Read More »Ambaliyar Borno: Gwamnatin Tarayya Zatai Aiki Da Ƙungiyoyi Wajen Tallafawa Al’ummar Maiduguri
Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja. Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙudiri Aniyar yin aiki da ƙungiyoyin Sa-kai, domin tallafawa al’ummar da Ambaliyar ruwa ta mamaye gidajensu, a Maidugurin Jihar Borno dake Arewa maso gabashin ƙasar. Maitaimaki na Musamman ga mataimakin Shugaban ƙasa kan harkokin shari’a, Barista Bashir Maidugu ne ya sanar da hakan, a yayin da yake karɓar kayayyakin tallafi daga …
Read More »Ambaliya Maiduguri : Jarman Sokoto Da Ɗan Iyan Jarma, Sun Bada Tallafin Kayan Milyan 30
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal. Mai Girma Jarman Sokoto Dakta Ummarun Kwabo (Uban Marayu), da kuma Ɗan iyan Jarma Alhaji Murtala Abdul Ƙadir, sun bada tallafin kayan abinci na sama da Naira Milyan 30 ga waɗanda Iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maidugurin Jihar Borno. Sadaukin Sokoto Malam Muhammad Lawal Maidoki, da kuma Shugaban Hukumar Zakka da wakafi ta …
Read More »