Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Tsohon Shugaban Hukumar tsaron Al’umma ta Civil Defence, Abdullahi Gana Muhammad, ya shawarci Majalisar Dattawan Najeriya ta samar da tsarin da zai inganta sashen yaƙi da matsalar Gonaki da Makiyaya na Civil Defence domin ya haɗa aikin gaba-ɗaya, maimakon ƙudirin samar da wata sabuwar hukumar yaƙi da satar Ma’adanai. Gana Muhammad na wannan tsokaci ne …
Read More »Tag Archives: Borno
Masu Hannu Da Shuni Ku Ƙara Taimakawa Al’ummar Maiduguri – David Sabo Kentai
Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Tsohon Darakta a hukumar raya yankin Arewa maso gabashin Najeriya, Chief David Sabo Kentai, ya buƙaci masu hannu da shuni da su ƙara ƙaimi wajen taimakawa al’ummar da Ambaliyar ruwan ta shafa a Maidugurin jihar Borno. Kentai yayi wannan kiran ne, a yayin da yake miƙa saƙon sa na jaje ga gwamnati da …
Read More »Ambaliyar Borno: Gwamnatin Tarayya Zatai Aiki Da Ƙungiyoyi Wajen Tallafawa Al’ummar Maiduguri
Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja. Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙudiri Aniyar yin aiki da ƙungiyoyin Sa-kai, domin tallafawa al’ummar da Ambaliyar ruwa ta mamaye gidajensu, a Maidugurin Jihar Borno dake Arewa maso gabashin ƙasar. Maitaimaki na Musamman ga mataimakin Shugaban ƙasa kan harkokin shari’a, Barista Bashir Maidugu ne ya sanar da hakan, a yayin da yake karɓar kayayyakin tallafi daga …
Read More »Ambaliya Maiduguri : Jarman Sokoto Da Ɗan Iyan Jarma, Sun Bada Tallafin Kayan Milyan 30
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal. Mai Girma Jarman Sokoto Dakta Ummarun Kwabo (Uban Marayu), da kuma Ɗan iyan Jarma Alhaji Murtala Abdul Ƙadir, sun bada tallafin kayan abinci na sama da Naira Milyan 30 ga waɗanda Iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maidugurin Jihar Borno. Sadaukin Sokoto Malam Muhammad Lawal Maidoki, da kuma Shugaban Hukumar Zakka da wakafi ta …
Read More »Ambaliyar Maiduguri : Rundunar ‘Yan Sandan Borno Ta Bada Wasu Shawarwari
Daga Bashir Gasau. Rundunar ‘Yan Sandan jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Kwamishina CP ML Yusufu, ba bawa al’ummar jihar wasu shawarwari biyo bayan faruwar ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri. Jami’n dake kula da masu magana da yawun Rundunar a Arewa maso gabas, SP Ahmed Mohammed Wakil ne ya sanar da hakan ta cikin wata …
Read More »Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Borno Ta Fitar Da Jadawalin Waɗanda Suka Bada Tallafi
Daga Bashir Gasau. Gwamnatin jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum, ta fitar da Jadawalin waɗanda suka bada tallafin tallafi, akan iftila’in ambaliyar da ta faru a birnin Maiduguri. Mashawacin Gwamnan akan yaɗa labarai Abdurrahman Ahmed Bundi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda …
Read More »Ambaliyar Maiduguri : Sarkin Kano Na 15 Ya Miƙa Saƙon Jaje Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa
Daga Bashir Gasau. Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya miƙa saƙon jaje ga al’ummar Maidugurin Jihar Borno, a bisa Iftila’in ambaliyar ruwan da ya same su. Sarkin ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran sa, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya aiko …
Read More »Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Bada Tallafin Naira Milyan 250 Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa
Daga Bashir Gasau. Gwamnatin Jihar Bauchi ta bada tallafin Naira Milyan 250, ga waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maidugurin Jihar Borno. Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ne ya tabbatar da hakan, a yayin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar domin zuwa ziyarar jaje, ga Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum dama al’ummar …
Read More »Ambaliyar Maiduguri : Ƙungiyar Bilal Charity Care Foundation Ta Tallafawa Waɗanda Iftila’in Ya Shafa
Daga Aliyu Gerengi, Gombe. Gidauniyar dake tallafawa Marayu da marasa ƙarfi ta jihar Borno wato Bilal Charity Care Foundation (BCCF), ta tallafawa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a birnin Maiduguri. Shugaban Gidauniyar na jihar Kwamared Bilal Muhammad Ali Biu ne ya bayyana hakan, a yayin da tawagar ƙungiyar ta ziyarci ɗaya daga cikin wuraren …
Read More »Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Kano Ta Bada Tallafin Naira Milyan Ɗari Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa
Daga Bashir Gasau. Gwamnatin Jihar Kano ta bada tallafin Naira Milyan ɗari, ga waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maidugurin Jihar Borno. Tawagar Gwamnatin Kanon ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan yaɗa Labarai, Baba Halilu Dantiye ne suka miƙa takardar Cakin Kuɗin ga Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a yayin ziyarar jajen da suka kai jihar. …
Read More »