Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja. Cibiyar Dake bibiyar yadda ‘Yan Majalisu da sauran hukumomin gwamnati ke kashe kudadensu, wato Connected Development, the followed the money (CODE), ta ce mahukuntan Najeriya sun gaza sauke nauyin da talakawan ƙasar suka ɗora musu, ta hanyar zaɓar su a matsayin Shugabanni. Shugaban Cibiyar CODE na Duniya Malam Hazmat Lawal ne ya bayyana hakan, a …
Read More »Tag Archives: Gwamnati
Gwamnati Zata Kashe Milyan 366, Domin Cike Ramukan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
Daga Jazuli Zakari Panshekara. Gwamnatin Najeriya ta ce ta amince da kashe naira Milyan 366, domin gudanar da gyare-gyare a hanyar Abuja zuwa Kaduna. Babbar hanyar, wadda Kamfanin Julius Berger ke sake ginawa tun kusan shekaru shida da suka gabata, tana fama da ramuka da sauran matsalolin da suke tayar da hankalin Direbobi, kamar yadda jaridar …
Read More »Gwamnatin Kano Ta Tallafawa Masu Lalurar Laka Da Kayan Kula Da Lafiyarsu
Daga Rabi’u Usman, Kano. Sama da kayan Naira Milyan Bakwai Gwamnatin jihar kano ta bawa ƙungiyar masu lalurar Laka, domin su ci-gaba da kula da lafiyar su albarkacin ranar masu larurar laka ta duniya dake tafe. Kwamishiniyar ma’aikatar Mata, ƙananan yara da masu buƙata ta musamman, Hajiya Aisha Lawan Saji Rano ce ta …
Read More »Inganta Sashen Kula Da Satar Ma’adanai Na NSCDC Yafi Ƙirƙiro Sabuwar Hukuma – Gana Muhammad
Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Tsohon Shugaban Hukumar tsaron Al’umma ta Civil Defence, Abdullahi Gana Muhammad, ya shawarci Majalisar Dattawan Najeriya ta samar da tsarin da zai inganta sashen yaƙi da matsalar Gonaki da Makiyaya na Civil Defence domin ya haɗa aikin gaba-ɗaya, maimakon ƙudirin samar da wata sabuwar hukumar yaƙi da satar Ma’adanai. Gana Muhammad na wannan tsokaci ne …
Read More »‘Yancin Kai: Gwamnan Kano Ya Ɗauki Nauyin Kula Da Rayuwar Marayu 95
Daga Bello Usman. A ƙoƙarin sa na nuna halin Karamci da tausayi, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki nauyin kula da rayuwar marayu 95 da ke jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata liyafar cin abinci tare da yaran, waɗanda suke zaune a gidan marayu na jihar …
Read More »Budaddiyar Wasika Ga Gwamnatin Najeriya (An Bar Jaki Ana Dukan Taiki Akan Lafiya)
Daga Bashir Gasau. Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Cikin girmamawa gareku shuwagabanni da Jami’o’in lafiyar na kasa ta Najeriya baki daya. Na ɗauki alkalami na ne domin nayi kira gareku akan wani ganganci da kantafi da rayukan al’umma da naga hukumar haraji ta Najeriya tayi a wani asibiti mai zaman kansa a birnin …
Read More »‘Yancin Kai: Gina Najeriya Nauyi Ne Akan Kowanne Ɗan Ƙasa – Chidari
Daga Bashir Gasau. Wakilin Al’ummar Dambatta da Makoda a Majalisar Wakilan Najeriya, Rt. Honarabul Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya bayyana batun gina Najeriya a matsayin abinda ya ke wuyan kowanne ɗan ƙasar ba iya shugabanni ba. Chidari na wannan bayani ne ta cikin saƙon taya murna ga al’ummar Najeriya, dangane da zagayowar …
Read More »Mun Shirya Wasan Dambe Domin Murnar Samun ‘Yancin Kai – Kwamared Murtala Gamji
Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja. Shugaban ƙungiyar Dattawan Matasan arewacin Najeriya, Kwamared Murtala Garba (Gamji), ya fara zagayen murnar ranar samun ƴancin kai, wanda ya kasance karo na 64. Gamji, wanda shine tsohon Shugaban Majalisar Matasa ta ƙasa wato (NYCN), ya fara zagayen ne da shirya wasan damben gargajiya ga ɗaukacin Matasan Arewacin Najeriya, domin murnar zagayowar ranar samun Yancin …
Read More »Hukumar NCAOOSCE Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Haɗa Kan Ƙungiyoyin Makarantun Allo
Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Hukumar dake kula da ilimin Almajirai da Yara da basa zuwa Makaranta ta Najeriya wato NCAOOSCE atakaice, ta kaddamar da kwamiti da zai hada kan kungiyoyin makarantun allo na kasa domin samar da kungiya daya wadda za ta rika mu’amala da ita a madadin dukkanin kingiyoyin. Shugaban hukumar ta NCAOOSCE Dakta Muhammad Sani Idiris …
Read More »Muna Da Yaƙinin Rahoton Kwamitin Jega Zai Magance Matsalar Rikicin Fulani – MACBAN
Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja. Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN), ta bayyana ƙwarin gwuiwar da take dashi akan rahoton kwamitin Farfesa Jega, na magance rikicin dake faruwa a tsakanin Makiyaya da kuma Manoma. Shugaban ƙungiyar MACBAN na Najeriya, Baba Usman Ngelzarma ne ya bayyana hakan, a yayin zantawar sa da jaridar GTR Hausa a Abuja, inda …
Read More »