Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Shugaban Ƙungiyar Miyatti Allah Kautal Hore ta Najeriya, Alhaji Bello Abdullahi Baɗejo, ya bayyana Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad a matsayin Mutumin kirki. Abdullahi Baɗejo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da jaridar GTR Hausa a ofishinsa dake kan hanyar Abuja zuwa Keffi, albarkacin cikar Gwamnan shekaru 66 da haihuwa. A …
Read More »Tag Archives: Sanata Bala Muhammad
Awanni 48 Na Bawa Gwamnatin Bauchi Ta Janye Kalamanta Ko Mu Tafi Next Level – Ɗan Bello
Daga Bashir Gasau. Fitaccen ɗan Barkwancin nan Bello Galadanci (Ɗan Bello), ya bawa Gwamnatin jihar Bauchi wa’adin awanni 48 ta janye kalaman da tayi a kansa kuma ta bashi haƙuri. Ɗan Bello ya sanar da hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce matuƙar ba …
Read More »Kansar Ƙwaƙwalwa : Gwamnan Bauchi Ya Tallafawa ‘Yar Jarida Domin Neman Lafiyar Ta
Daga Bashir Gasau. A ƙoƙarin sa na nuna tausayi da shugabanci na gari, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bada tallafin Naira Milyan 5 ga wata ‘yar jarida, domin jiyyar ta akan lalurar Kansar Ƙwaƙwalwa a Asibitin Ƙwararru na Jami’ar Jos dake jihar Plateau. Mai bawa Gwamnan shawara kan yaɗa labarai Kwamared …
Read More »Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Bada Tallafin Naira Milyan 250 Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa
Daga Bashir Gasau. Gwamnatin Jihar Bauchi ta bada tallafin Naira Milyan 250, ga waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maidugurin Jihar Borno. Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ne ya tabbatar da hakan, a yayin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar domin zuwa ziyarar jaje, ga Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum dama al’ummar …
Read More »Kisan Zaranda : Gwamnatin Jihar Bauchi Tayi Allah-Wadai Da Kalaman Sanata Shehu Buba
Daga Aliyu Gerengi, Gombe. Gamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sanata Bala Muhammad, ta yi Allah-Wadai da kalaman Sanatan Bauchi ta kudu Senator Shehu Buba. Na zargin Ma’aikatan hukumar Sintirin jihar da hannu wajen kisan da ya faru a ƙauyen Zaranda dake ƙaramar hukumar Toro. Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na jihar Abubakar …
Read More »