Daga Bashir Gasau. Ofishin babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman a yankin Sahel, ya ce ya fara wata tattaunawa ta musamman domin nemawa yankin Sahel mafita a karo na biyu. Tattaunawar za ta maida hankali ne akan hanyoyin da za’a magance matsalolin da suka addabi yankin, kamar yadda aka ƙaddamar da …
Read More »Tag Archives: Tallafi
Masu Hannu Da Shuni Ku Ƙara Taimakawa Al’ummar Maiduguri – David Sabo Kentai
Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Tsohon Darakta a hukumar raya yankin Arewa maso gabashin Najeriya, Chief David Sabo Kentai, ya buƙaci masu hannu da shuni da su ƙara ƙaimi wajen taimakawa al’ummar da Ambaliyar ruwan ta shafa a Maidugurin jihar Borno. Kentai yayi wannan kiran ne, a yayin da yake miƙa saƙon sa na jaje ga gwamnati da …
Read More »Ambaliya Maiduguri : Jarman Sokoto Da Ɗan Iyan Jarma, Sun Bada Tallafin Kayan Milyan 30
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal. Mai Girma Jarman Sokoto Dakta Ummarun Kwabo (Uban Marayu), da kuma Ɗan iyan Jarma Alhaji Murtala Abdul Ƙadir, sun bada tallafin kayan abinci na sama da Naira Milyan 30 ga waɗanda Iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maidugurin Jihar Borno. Sadaukin Sokoto Malam Muhammad Lawal Maidoki, da kuma Shugaban Hukumar Zakka da wakafi ta …
Read More »Attahiru Bafarawa : An Ƙaddamar Da Kwamitin Rabon Naira Bilyan Guda Ga Sakkwatawa
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal. Gidauniyar tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Dakta Attahiru Bafarawa, ta ƙaddamar da kwamitin da zai jagoranci rabon tallafin Naira Bilyan guda ga Sakkwatawan dake faɗin jihar. Tsohon Gwamnan Jihar Dakta Attahiru Bafarawa ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin, inda ya ce ya bada tallafi ga mutanen jihar ne domin rage musu raɗaɗin talaucin da suke …
Read More »Zamu Ƙwato Haƙƙin Waɗanda Shari’arsu Tayi Nuƙusani Babu Dalili – Legal Aid Council
Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Hukumar bayar da agajin Shari’a kyauta ta Najeriya wato (Legal Aid Council), ta sha alwashin ci-gaba da aiwatar da ayyukan ta na ƙwato haƙƙin waɗanda shari’ar su ke nuƙusani ba tare da wani dalili Mai ƙarfi ba. Shugaban hukumar na Najeriya Barista Aliyu Abukabakar Gwandu ne ya sanar da hakan, a yayin zantawarsa da …
Read More »Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Borno Ta Fitar Da Jadawalin Waɗanda Suka Bada Tallafi
Daga Bashir Gasau. Gwamnatin jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum, ta fitar da Jadawalin waɗanda suka bada tallafin tallafi, akan iftila’in ambaliyar da ta faru a birnin Maiduguri. Mashawacin Gwamnan akan yaɗa labarai Abdurrahman Ahmed Bundi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda …
Read More »Kansar Ƙwaƙwalwa : Gwamnan Bauchi Ya Tallafawa ‘Yar Jarida Domin Neman Lafiyar Ta
Daga Bashir Gasau. A ƙoƙarin sa na nuna tausayi da shugabanci na gari, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bada tallafin Naira Milyan 5 ga wata ‘yar jarida, domin jiyyar ta akan lalurar Kansar Ƙwaƙwalwa a Asibitin Ƙwararru na Jami’ar Jos dake jihar Plateau. Mai bawa Gwamnan shawara kan yaɗa labarai Kwamared …
Read More »